Shugaban kasar Ugandan Yoweri Museveni, wanda shi ne babban mai shiga tsakani ya jagoranci taron a fadar gwamnati ta Entebbe, wanda ke da tazarar kilomita 40 a kudu da Kampala babban birnin kasar.
Tattaunawar karkashin jagorancin kungiyar kasashen yankin gabashin Afrika, wanda ya hada da kasashen Uganda, da Rwanda, da Burundi, da Kenya da kuma Tanzaniya.
Kadan daga cikin muhimman abubuwan da za'a tattauna sun hada da kafa gwamnatin hadin kan kasa, da kuma samar da tsaro a kasashen.
Manazarta suna hasashen za'a tattauna batun tura dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afrika AU zuwa kasar Burundi.
A cewar gwamnatin Ugandan, an dauki dogon lokaci ba'a gudanar da tattaunawar ba, sakamakon ra'ayoyin da aka bayyana dangane da alfanun da tattaunawar za ta haifar.
Rikicin kasar Burundi, ya barke ne a watan Aprilun wannan shekara, tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza na kasar, ya nemi zarcewa a mulki a karo na uku. Matakin da ya haifar da zazzafar adawa daga al'ummonin kasar, bisa kafa hujjar cewar ya ci karo da dokar kundin tsarin mulkin kasar.(Ahmad Fagam)