in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda ya nuna yabo ga Sin kan taimakon da Sin ta samar wa kasarsa wajen gina ababen more rayuwa
2015-08-30 17:38:23 cri
Jiya asabar 29 ga wata, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya bayyana cewa, kasarsa na dukufa wajen gina ababen more rayuwa, tare da nuna matukar godiya game da taimakon da kasar Sin ta baiwa kasarsa wajen gina ababen more rayuwa.

Mr. Museveni ya bayyana haka ne a yayin da yake halartar bikin fara aikin fadada filin jiragen sama na Entebbe dake kudancin birnin Kampala, inda kuma ya bayyana cewa, bunkasuwar kasashen Afirka na bukatar kyawawan ababen more rayuwa, kuma aikin fadada filin jiragen saman Entebbe zai kara kyautata ababen more rayuwa na kasar da kuma gaggauta cigaban tattalin arzikin kasar, haka kuma, kasarsa na gode wa Sin matuka dangane da babban taimakon da ta samar mata a wannan fanni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China