Da yake karin haske game da hakan, shugaban rundunar sojin kasar Uganda Janar Edward Katumba Wamala, ya ce kayayyakin da Sin ta samar za su tallafa matuka wajen aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia. Janar Wamala ya kara da cewa wannan aiki na matukar bukatar kayayyakin aiki, don haka samar da irin wannan taimako abu da ake matukar bukata.
Kasar Uganda dai ta tura dakarun ta har 8,000 zuwa Somalia, karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU.