A wannan rana, a yakin neman zabe da aka yi a birnin Kampala hedkwatar kasar, Museveni ya ce, za'a hukunta duk wanda aka samu da hannu a yunkurin tada zaune tsaye a lokacin babban zabe. Ya ce, ya zama wajibi a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin zaben, wanda ake saran zai taimaka wajen raya kasa da ma ci gaban kasar baki daya.
Kafin jawabin na Museveni, bangaren 'yan sanda da masu goyon baya ga jam'iyyar adawa ta kasar sun yi rikici a cibiyar babban birnin kasar, abin da ya haddasa mutuwar mutum guda da jikkatar wasu da dama.
Yayin da babban zaben kasar Uganda ke karatowa, an kara tura jami'an tsaro a birnin Kampala da sauran wuraren kasar, kuma sojoji da dakaru suna yin sintiri a wadannan wurare don magance sake aukuwar rikici.(Bako)