Firaministan kasar Uganda Ruhakana Rugunda, ya shaidawa manema labarai cewa, akwai bukatar samun cikakkiyar fahimtar juna tsakanin sassan 'yan adawar kasar Burundi, gabannin ci gaba da tattaunawa da nufin kawo karshen tirka tirkar siyasar da ta addabi kasar. Mr. Rugunda ya ce daukar wannan mataki zai taimaka, wajen gudanar shawarwari cikin sauki da kuma nasara.
A ranar 28 ga watan Disambar da ya shude ne dai mambobin kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka, suka zabi shugaba Yoweri Museveni na Uganda, a matsayin babban mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar ta Burundi.
A daya bangaren kuma kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta ayyana kudurin ta na tura dakaru 5,000 zuwa kasar Burundin, domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya da dakatar da bude wuta, yayin da tattaunawa ke gudana.
Tun dai cikin watan Afrilun shekarar bara ne fada ya barke a kasar ta Burundi, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya ayyana nufinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, matakin da dama daga 'yan kasar ke kallo, a matsayin sabawa kundin tsarin mulkin kasar.(Saminu Alhassan)