Wadannan 'yan ta'addanci sun kona gidaje fiye da 300 tare da yin garkuwa da mazauna kauyukan. Rundunar tsaro da masu aikin sakai, sun gano gawawwaki 85 a wuraren da lamarin ya faru, sannan ana ci gaba da kula da wadanda suka samu raunuka a asibiti.
Rahotanni na cewa, sojojin kasar sun yi musayar wuta da mayakan na tsawon sa'o'i 4, yanzu haka hankulla sun fara kwantawa a yankunan da lamarin ya faru. Sai dai har ya zuwa yanzu, babu wata kungiya data yi ikirarin daukar alhakin kaddamar da hare haren. (Amina)