Shugaba Mhammadu Buhari ya yi wannan sanarwa a ranar Talata a birnin Abuja a fadar shugaban kasar a yayin ziyarar Jin-Yong Cai, darekta janar na kamfanin kudin kasa da kasa (IFC), wata babbar hukumar kasa da kasa da ta kware a fannin cigaban bangaren masu zaman kansu da kuma yaki da talauci, da ke cikin gungun bankin duniya.
Kawo sauye sauye a kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya kasance dole ganin yadda ya yi fama da hanci da wuce doka da oda a halin yanzu a tsawon shekarun da suka wuce, in ji shugaba Buhari.
Haka kuma, shugaban Najeriya ya bayyana wajabcin mai da hankali da darajanta kudaden shiga da ake samu daga kowane kamfani a matsayin wata karin dama na karfafa kawo gyara na NNPC.
Gwamnati na cigaba da yin kokari sosai domin kara samun kudin shiga ta yadda hukumomin kasar zasu iya aiwatar shirinsu yadda ya kamata na kawo sauyi da kara kyautata zaman rayuwar 'yan Najeriya, in ji shugaba Buhari. (Maman Ada)