in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: Bincike kan sayan makamai ya kai har ga manyan sojoji
2016-01-17 13:22:04 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayar da umurni ga hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gudanar da bincike mai zurfi kan muguwar halayyar wasu manyan sojoji dake kan aiki ko suka yi ritaya, game da wasu takardun sayan makamai.

Umurnin ya bayo bayan wata bukatar kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike kan yadda aka sayi makamai da kayayyakin soja da kuma bangaren tsaro daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015, in ji Garba Shehu, kakakin fadar shugaban kasa, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta (EFCC) ta kuma samu umurnin gudanar da bincike kan rawar da wasu shugabanni, kamfanoni da hukumominsu suka yi a cikin wadannan harkoki, bayan kwamitin bincike ya gabatar da wani rahoto na biyu.

Kurakurai da kwamitin binciken ya gano, a cewar wannan sanarwa sun kunshi rashin tantance kudaden da aka kashe wajen sayan makamai, rashin yarjejeniyoyi na kwangila, bayar da kwangila fiye da yadda gwamnati ta tsaida, tura kudade zuwa mutanen da ba a tantance su ba da kuma rashin girmama dokokin kasuwanci kamar yadda doka ta tanada.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da yaki da cin hanci tun bayan kama aikinsa.

Ginin tsaron Najeriya ya fuskanci matsaloli dalilin hare haren ta'addanci na baya bayan nan da kuma illar da za ta iya shafar muhimman bangarorin tattalin arziki.

Kwamitin bincike na fadar shugaban kan badakalar sayan mamakai ya bayyana a cikin wani rahotonsa ya gano cewa gwamnatin da ta shude ta wasa da kudin kasa fiye da kima, wannan kuma a karkashin Dasuki, wani kanal mai ritaya.

Hukumar EFCC tana zargin kanal Dasuki da sama da fadi da kudin da aka ware wajen sayan makamai da kayayyakin soja domin yin amfani da su wajen yakin neman sake zaben shugaba Goodluck Jonathan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China