in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maharan Boko Haram sun hallaka mutane 5 a arewa maso gabashin Najeriya
2016-01-12 10:48:08 cri

Wasu 'yan bindiga masu dauke da makamai da ake zaton 'yan Boko Haram ne a daren Lahadin da ta gabata sun afkawa wani kauye dake wajen garin Madagali a jihar Adamawa dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda suka hallaka mutane 5, sannan suka cinna wa wasu gidaje wuta.

Wannan dai shi ne hari na farko da garin ya fuskanta a wannan shekara, a jerin hare-haren da yankin na Madagali ke fuskanta, tun bayan wani harin kunar bakin wake a ranar 28 ga watan Disambar 2015, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane 17, sannan wasu 41 suka jikkata.

Abu Malik, wani mazaunin kauyen ne, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, harin ya afku ne da misalin karfe 11 na yammacin Lahadi.

Adamu Kamale, dan majalisar tarayya mai wakiltar Madagali/Michika, ya yi Allah wadai da wannan hari, sannan ya bukaci a samar da karin jami'an tsaro a yankin.

Wannan hari dai, ya zo ne kwanaki biyar bayan da mazauna yankin da jami'an gwamnati suka yi kira a tura karin sojoji a yankin na Madagali. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China