Olabisi Kolawole, kakakin hukumar ta kasar, ta tabbatar da hakan ne ga kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, tuni hukumar 'yan sandan kasar ta umarci mataimakin babban sifeton 'yan sandan kasar mai kula da shirin sintiri na Sotonye Wakama, da ya jagoranci tawagar 'yan sandan farin kaya domin gudanar da aikin bincike a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Wannan mataki ya kasance tamkar share fage ne na yunkurin tura jami'an 'yan sandan dubu 3 zuwa yankin don samar da tsaro.
Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Solomon Arase, ya ce manufar tura jami'an 'yan sandan shi ne, don tallafawa sojojin kasar dake yankin.
Arase, ya ce za'a tura jami'an 'yan sandan tare da kayan aiki domin ba da kariya ga 'yan gudun hijira wadanda ke komawa garuruwan su.
Sannan ya bukaci masu ruwa da tsaki, musamman 'yan jaridu da su taimakawa hukumomin tsaro don samun dawwamamman zaman lafiya a tsakanin al'ummomin kasar.(Ahmad Fagam)