Gwamnatin kasar Najeriya ta sanar a daren ran 8 ga wata cewa, kawo yanzu kasar ta samu mutane 86 da suka kamu da cutar Lassa, kuma 40 daga cikinsu sun rasa rayukansu.
Ministan kiwon lafiya na kasar Farfesa Isaac Adewole ya kira wani taron manema labaru a birnin Abuja hedkwatar kasar a daren wannan rana cewa, kawo yanzu an gano wannan cuta a jihohi 10 daga cikin jihohi 36 na kasar. A cewarsa, gwamnatin ta dauki matakan gaggawa don yin rigakafi da magance cutar, inda ta tura rukunonin tinkarar matsalar zuwa jihohin da aka gano cutar don taimakawa wadanda suka kamu da cutar, da bincike kan wadanda suka taba tuntubar wadanda suka kamu da cutar.
Ban da wannan kuma, Adewole ya gargadi iyalan wadanda suka kamu da cutar da masu aikin kiwon lafiya da kada su taba jini ko ruwan jikin wadanda suka kamu da cutar. Kuma ya ba da shawara ga jama'a da su kyautata halin lafiya da ake ciki da mai da hankali kan ingancin abinci, da kaucewa abincin da beraye suka gurbata da fitsari ko kashin bera.
Dadin dadawa, Adewole ya ce, cutar ta bulla ne a wannan karo a watan Nuwamban bara. Sai kuma a shekarar 2012, cutar Lassa ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40, wadda kuma ta shiga jihohi har 12. (Amina)