in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bincike ga kaji 24,000 a wata jihar a arewacin Najeriya saboda murar tsuntsaye
2016-01-21 10:29:49 cri
Fiye da kaji 24,000 ne aka ma bincike a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya sakamakon bullar murar tsuntsaye a jihar, kamar yadda wani jami'i a sashin kula da kiwon dabbobi yayi bayani.

Tsuntsayen sun hada da kaji 24,000,Zabi 456,dawisu 250 da talotalo 54, inji Kwamishinan kula da kiwon dabbobi a jihar Isa Salihu, wanda ya bayyana ma kamfanin dillancin labaru na Xinhua haka a garin Yola.

Gonakin kiwon tsuntsayen da hakan ya shafa duk an killace su sannan ana daukan matakan da ya dace na hana yaduwan cutar .

Jami'in ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta fara aiwatar da yekuwa na fadakar da jama'a na kada su taba duk wassu kajin da suka mutu kuma kada su dafa wanda aka yanka sakamakon rashin lafiya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China