Rahotanni daga Najeriya na cewa, a yau Laraba ne ake sa ran shugaba Buhari na Najeriyar zai kai ziyarar aiki ta kwanaki uku kasar Kenya da nufin kara karfafa dangantaka da harkokin cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ta Najeriya Manoah Esipisu ya rabawa manema labarai, ta bayyana cewa, shugaban na Najeriya zai gana da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta, inda za su tattauna kan harkokin cinikayya, yawon shakatawa da aikin gona, kafin daga bisani su zarce zuwa barakin sojoji na Moi da ke Eldoret inda za su hade da takwaransu na kasar Habasha a wani taron addu'o'i na musamman da aka shirya don tunawa da dakarun kasar da aka halaka a kasar Somaliya.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ce kasashen biyu suka amince da kafa hukumar dangantaka ta hadin gwiwar, da nufin karafa hadin gwiwa a fannonin cinikayya, ilimi, makamashi, yawon shakatawa, da fasahohi.
Bayanai na nuna cewa, sakamakon bunkasuwar cinikayya tsakanin Kenya da Najeriya ta sa jiragen kasar Kenyan na zirga-zirga a biranen Najerya.(Ibrahim)