Air Marshall Abubakar Sadique, ya ce an gina filin jirgin ne a jihar Naija, kuma ana sa ran hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihar ta Naija, da ma sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da cin gajiyar sa.
Sadique ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gwamnan jihar Naija Abubakar Sani Bello a birnin Abuja fadar mulkin Najeriyar. Ya kuma kara da cewa, rundunar sojin saman kasar na daukar matakan da suka wajaba na tabbatar da tsaro a jihar ta Naija, ta hanyar tura dakarun hukumomin tsaro da ake bukata.
Da yake maida jawabi game da wannan batu, gwamna Abubakar Bello, cewa ya yi gwamnatin sa na duba dukkanin sassan da ya dace na yin hadin gwiwa da rundunar sojin saman kasar, domin fadada kwarewa ma'aikatar ta a fannin samar da tsaro, musamman a kewayen sabon filin jirgin. Ya ce samar da wannan filin saukar jirage masu saukar ungulu, zai bunkasa harkokin tattalin arzikin jihar ta Naija, baya ga karfafa harkokin tsaro. (Saminu Alhassan)