Wani jami'in hukumar tsaro da ceto rayukan al'umma ya ce, a kalla mutane 12 ne aka ba da rahoton mutuwarsu a sakamakon harin kunar bakin wake a garin Chibok dake jahar Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Jami'in mai suna Hassan Chibok, kuma shugaban tawagar jami'an kai daukin gaggawa ya fada cewar, tawagar tasu ta samu gawawwakin mutane 12, amma a cewarsa adadin zai iya zarta hakan. Ya kara da cewar mutanen da suka samu raunuka a harin adadinsu ya kai 28.
Wasu jami'an tsaro su shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, wasu 'yan kunar baki su 5 ne suka shiga garin na Chibok a ranar kasuwar garin, sai dai mutane uku ne daga cikin maharan ake zargi su tada bama baman, lamarin da ya jefa garin cikin yanayi na rudewa.
Sai dai jami'an tsaron sun ce, ragowar maharani biyu da ake zargi sun sulale ba'a gan su ba.
A garin na Chibok ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan sakandare kimamin 200 a watannin 21 da suka wuce.(Ahmad Fagam)