Babban jami'in hukumar kula da hannayen jarin kasar Oscar Onyema ne ya yi wannan bayani yayin taron bitar yanayi kasuwar hannayen jari na 2015 da kuma yadda kasuwar za ta kasance a shekarar 2016.
Jam'in ya kuma bayyana cewa, canje-canjen da aka samu a kasuwannin hannayen jarin kasar, sun biyo bayan sabbin manufofin kasar, da hasashen da ta ke na samun ci gaba, da batun tsaro da kuma matakan da kasar ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa, gami da yawan kayayyakin da ake fatan shigo da su cikin kasar.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, kasuwar hannayen jarin kasar, za ta iya taimakawa wajen cike gibin kasafin kudin kasar ta Najeriya na 2016.
Jami'in hukumar NSE ya kuma bayyan cewa, harajin da kasar ta ke samu ya ja baya, sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, rashin tabbas a harkar siyasa da tattalin arzikin kasar, sakamakon babban zaben da aka gudanar a kasar a watan Afrilun shekarar 2015.
Don haka ya ce, hukumarsa za ta yi kokarin bullo da matakan da za su bunkasa tattalin arzikin kasar.
An gudanar da taron hukuma na wannan karo ne a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar ta Najeriya.(Ibrahim)