Ibrahim Abubakar, mai shekaru 43, shi ne jami'i mai kula da tsare tsare a hukumar ta NFF.
A wata sanarwa da hukumar ta NFF ta fitar, ta bayyana matukar juyayi dangane da mutuwar jami'in nata.
A wata sanarwar ta dabam, babban sakataren NFF Mohammed Sanusi , ya bayyana marigayi Abubakar a matsayain hazikin ma'aikaci mai sanin ya kamata.
Tuni dai jami'an tsaro a kasar suka tabbatar da aniyar su na zakulo wadanda ke da hannu wajen hallaka jami'in. kuma bincike na farko farkon nan ya nuna cewar, maharan, sun balle gidan Abubakar ne, kuma suka bude masa wuta nan take.(Ahmad Inuwa Fagam)