Babban masanin ilmin tattalin arziki mai ba da shawara na wannan banki Mista Jan Hatzius ya bayyana a wani dandalin tattaunar manyan tsare-tsaren kasar Sin da aka yi a wannan rana a nan birnin Beijing cewa, raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba zai kawo mummunan tasiri ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya sosai ba, musamman ma ga kasashe masu wadata. A cewarsa, Amurka da kasashe dake yin amfani da kudin Euro ba za su fuskanci hadarin ciniki mai tsanani dangane da kasar Sin ba. A wani hannu na daban, Sin ba ta da alaka mai zurfi da tsarin hada-hadar kudi na kasashen Turai da Amurka. A don haka, raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba zai kawo mummunan tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki ba a fannin ciniki da hada-hadar kudi.
Game da saurin bunkasuwar tattalin arziki a shekarar bana da badi kuma, Goldman Sachs ya yi kiyasin cewa, adadin zai kai 6.9% a bana kuma 6.3% a badi, adadin da ya bayyana karfin samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri. (Amina)