Rhee Chang-yong a sharhinsa ya kara da cewa, duk da cewa harkokin kere-kere da gine-gine sun ragu a kasar Sin, amma jarin da aka zuba a bangaren ababen more rayuwa da kuma harkokin samar da hidimomi na ci gaba da karuwa cikin sauri a kasar, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin za ta iya rage dogaro da kayayyakin da ta ke fitarwa zuwa kasashen waje da kuma jarin da aka zuba mata, don ta gyara tattalin arzikinta ta yadda zai dace da manufofin harkokin saye da sayarwa da samar da hidimomi.(Lubabatu)