in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu ci gaba wajen kyautata salon raya tattalin arzikinta
2015-10-08 18:57:46 cri
Jaridar People's Daily ta wallafa wani sharhin da shugaban hukumar kididdigar kasar Sin Wang Bao'an ya rubuta mai taken "A kalli yawan wutar lantarki da ake amfani da shi, da yawan kayayyakin da ake sufurarsu ta jiragen kasa don ganin sabon ci gaba da aka samu ta hanyar kyautata salon raya tattalin arziki."

Sharhin ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, dangantakar da ke tsakanin raya tattalin arziki da yawan wutar lantarki da aka yi amfani da shi, da yawan kayayyakin da ake sufurarsu ta hanyar jiragen kasa ta jawo hankalin al'umma a gida da waje.

A cikin 'yan shekarun nan, an shiga sabon mataki na raya tattalin arzikin Sin, kana an samu sauye-sauye a kasar Sin game da dangantakar da ke tsakanin raya tattalin arziki da yawan wutar lantarki da ake amfani da shi da yawan kayayyakin da ake sufurarsu ta hanyar jiragen kasa. Abun da ya nuna cewa, yayin da aka samu raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki, a hannu guda kuma an samu raguwar yawan wutar lantarki da ake amfani da shi da dama, kana yawan kayayyakin da aka yi sufurar su ta hanyar jiragen kasa shi ma ya ragu sosai, wadannan sauye-sauye da aka samu ba ya nufin, tattalin arzikin Sin ya samu koma baya, kuma ba ya nufi, akwai kuskure game da alkaluman da aka samu, maimakon hakan, ya shaida cewa, Sin ta samu babban ci gaba game da canja salon raya tattalin arzikinta.

Dalilin da ya sa aka samu tafiyar hawainiya game da saurin karuwar yawan wutar lantarki da aka yi amfani da shi, shi ne sabo da sana'ar ba da hidimomi ta karu, kana an gaggauta canja salon bunkasuwar masana'antu, kuma yadda ake amfani da makamashi ya ingata matuka. A daya hannu kuma, dalilin da ya sa aka samu raguwar yawan kayayyaki da ake sufurar su ta jiragen kasa shi ne, an canja salon raya tattalin arziki, da kyautata salon amfani da makamashi, da sufurin kayayyaki ta hanyoyi da dama da dai sauransu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China