in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa ketare bai canja ba, in ji ma'aikatar cinikayyar kasar
2015-11-06 10:53:32 cri

Ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a wani rahoton da ta fitar jiya cewa, ana saran yawan kayayyakin da kasar Sin za ta fitar zuwa ketare a wannan shekara zai kasance kamar yadda ake fata, yayin da za a samu raguwar yawan kayayyakin da za a shigar cikin kasar.

Rahoton ma'aikatar ya kuma nuna cewa, cinikayyar kasar na ketare ya dan ragu kadan, idan aka kwatanta da alkaluman cinikayya na duniya da na galibin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya.

Bayanai na nuna cewa, a cikin watanni 4 na farkon wannan shekara cinikayyar ketara na kasar ya ragu zuwa Yuan triliyan 17.87 wato kashi 7.9 cikin bisa makamancin lokaci na bara. Yayin da kayayyakin da ake fitarwa zuwa ketare ya yi kasa da kashi 1.8 cikin 100 kimanin Yuan triliyan 10.24 kana kayayyakin da ke shigowa kasar su ma sun ragu da kashi 15.1 cikin 100 zuwa yuan triliyan 7.63.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, rarar cinikayyar kasar ta karu da kashi 82.1 cikin 100 wato yuan triliyan 2.61.

Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fama da yanayi mai sarkakiya da duniya ke fuskanta, koma bayan bukatar kawasunni, raguwar gasa da kuma karuwar tangardar cinikayya a shekara 2016.

Rahoton ya ce, kasar Sin tana iya hankoron saurin karuwar ci gaba fiye da matsakaicin hasashen da aka yi a duniya har ma ta samu gurbi a kasuwannin duniya, sakamakon manufofinta na bude kofa ga kasashen waje da kuma shirin nan na Ziri daya da hanya daya da kuma zurfafa yin gyare-gyare ga tsarin tattalin arzikin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China