Sabbin bangarori biyar da Sin ta inganta a sabon tsarinta na yau da kullum na tattalin arziki suna bayar da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, kuma Sin ta ci gaba da zama kasar dake sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Rahoton ya yi hasashen cewa, bunkasuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2015 ya kai kashi 3 cikin dari,kana a shekarar 2016 zai kai kashi 3.24 cikin dari, yayin da a shekarar 2017 zai kai kashi 3.43 cikin dari, wadanda ya yi kasa da zaton da aka yi a shekarar bara.
A bangaren kasar Sin kuwa, rahoton ya yi nuni da cewa, a shekarar da ta gabata, ko da yake saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ya dan ragu amma ya bunkasa cikin sauri. Ana kuma ci gaba kokarin kyautata tsari da tabbatar da ingancin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata. (Zainab)