Kakakin hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Li Pumin ya bayyana a gun taron manema labaru da hukumar ta shirya a yau cewa, a shekarar bara Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata, kuma an yi kiyasin cewa, saurin karuwar tattalin arizki a bara ya kai kashi 7 cikin dari, wanda ya yi daidai da hasashen da aka yi.
Mr Lin ya kuma yi hasashen cewa, a shekarar 2016, Sin tana da makoma mai haske da tushe mai kyau ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki, amma duk da haka, a sakamakon halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, akwai yiwuwar fuskantar wasu kalubaloli da wahalhalu da dama ta fuskar tattalin arziki. (Amina)