in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da tsarin yin kwaskwarima kan kamfanoni mallakar gwamnati
2015-09-14 13:31:39 cri

Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar shawara game da zurfafa kwaskwarima kan kamfanoni mallakar gwamnati, a jiya Lahadi 13 ga watan nan na Satumba, takardar da ta kasance mai matukar muhimmanci a wannan fanni.

Takardar mai kunshe da babi 8 da ayoyi 30, ta gabatar da muradun da za a cimma, da matakan da za a dauka a sabon matakin, bisa fannoni daban-daban a aikin yi wa kamfanoni mallakar gwamnatin kwaskwarima. Game da batun bunkasuwar kamfanonin hada-hadar hannun jari daban-daban da ake maida hankali a kan su kuwa, takardar ta nuna cewa kamata ya yi a yi amfani da jarin sassa masu zaman kansu, wajen kyautata ayyukan kamfanoni mallakar gwamnati, kuma kasar Sin tana fatan irin wannan jari zai shiga kamfanoni mallakar gwamnati ta hanyoyi daban-daban a kuma fannoni daban-daban.

Alal misali, akwai taimakawa wadannan kamfanoni wajen yin garambawul, da habaka jarin kamfanoni masu sayar da hannun jari, da fasahar sarrafa kamfanonin da dai sauransu. Ban da haka kuma, akwai batun gabatarwa kamfanoni masu jari daban-daban masu zaman kansu wasu ayyuka, wadanda suka dace da manufar masana'antu, da kawo moriya sosai a fannin kwaskwarima a fannoni daban-daban, ciki hadda na man fetur, da iskar gas, da wutar lantarki, da layukan jiragen kasa, da sadarwa, da makamashi, da harkokin jama'a da dai sauransu. Haka kuma akwai fannin gudanar da aikin gwaje-gwaje a wasu wurare game da hadin gwiwa tsakanin jarin gwamnati da jarin da na sassa masu zaman kansu, baya ga sa kaimi ga irin wannan hadin gwiwa tsakaninsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China