Ban da wannan kuma, Mista Stuart Gulliver ya ce, Sinawa na nuna karfi sosai wajen saye da sayarwa, kasuwar gidaje kuma na samun farfadowa bisa zagayowar lokaci, kuma an samu kyautatuwa a fannin manyan ababen more rayuwa, basussuka, hada-hadar kudi da sauransu. Dadin dadawa, tsarin da babban bankin kasar Sin ke dauka na canja tsai da darajar kudin Sin ya kasance wani babban mataki ne dake cikin kwaskwarima da Sin take yi, ba kamar jita-jita da aka yi ba wai da zummar rage darajar kudi ko sa kaimi ga sana'ar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ba. A cikin watanni da suka gabata, a cewar Mista Stuart Gulliver, sauyawar harkokin darajar kudi da kasuwannin hanayen jari cikin watannin da suka gabata ba za su kawo illa ga bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci ba. Bunkasuwar tattalin arziki da birane a kasar Sin zai samar da sabbin kasuwanni, kuma saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin zai haura bisa na bunkasuwar da duniya za ta samu. (Amina)