in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan karfin tattalin arzikin Sin a shekarar 2015 ya karu da kashi 6.9 cikin dari
2016-01-19 13:57:22 cri
Alkaluman kididdiga da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a Talatar nan sun nuna yadda yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar Sin wato GDP a shekarar 2015, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 67670.8, adadin da ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa na shekarar da ta gabace ta. Shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin Wang Baoan, ya bayyana hakan a wannan rana a nan birnin Beijing, yana mai cewa wannan karuwa ta kai matsayin koli a duniya, kuma adadin ya nuna yawan karuwar tattalin arzikin na kasar Sin ya kai kashi 25 cikin dari bisa na dukkan duniya.

Bisa wannan kididdiga, kasar Sin ta samu ci gaba a fannin karuwar samar da amfanin gona a shekarar ta 2015, inda yawan hatsi da ta samar a shekarar ya kai ton miliyan 621.43, adadin da ya karu da kashi 2.4 cikin dari sama da na shekarar 2014. Kana yawan masana'antu na kasar Sin ya samu karuwa sosai, inda yawan masana'antun sarrafa fasahohin zamani na kasar Sin ya karu da kashi 10.2 cikin dari bisa na shekarar 2014. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China