in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta inganta sassan da ke da raunin tattalin arziki
2015-12-21 20:07:31 cri

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na mayar da hankali kan sassan da ke raunin ci gaban tattalin arziki, ta hanyar fadada hanyoyin samar da kayayyaki.

Wannan na kunshe ne ciki wata sanarwar da aka bayar a karshen taron tsara manufofin kasar Sin na raya tattalin arziki da ya gudana a yau.

Taron ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don ganin an rage kaifin talauci, kara inganta fasahar kamfanoni, zakulo masu hakaza tare da inganta kwarewa game da aikin gona.

Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da dabarun da aka gano a bangaren kirkire-kirkire da yayyata abubuwan da masana'antu suka kirkiro.

Har ila a cewar taron, kasar Sin za ta kara mayar da hankali kan zurfafa yin gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki, ta yadda za a daidaita ci gaban tattalin arzikin kasa.

Bayanai na nuna cewa, aikin raya tattalin arzikin kasar Sin zai mayar da hankali kan fannoni guda biyar, wato rage kayayyakin da masana'antu ke samarwa, sassauta da kuma cike gibi, rage kudaden da masana'antu ke kashewa da daidaita raunin da ke akwai.

Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje ta hanyar inganta harkokin cinikayya, karfafa amfani da jarin waje da bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa kan yawan kayayyaki da na'urorin da za a rika samarwa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China