in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da kasar Sin ta jawo ya karu da 9% a farkon watanni 9 na bana
2015-10-13 18:41:21 cri

Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar ya nuna cewa, a farkon watanni 9 na wannan shekara, 'yan kasuwa baki sun zuba jari wajen kafa kamfanoni guda 18980 a fadin kasar ta Sin, wadanda yawansu ya karu da kashi 10.1 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Kana kuma jimlar jarin waje da aka yi amfani da shi ta kai kudin Sin RMB biliyan 584.74, wadda ta karu da kashi 9 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.

Wani jami'i a sashen kula da harkokin jarin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar ya bayana cewa, sana'ar ba da hidima ta fuskar fasahar zamani da kuma sana'ar kera kayayyaki na zamani sun ci gaba da kara jawo jarin waje a kasar Sin.

Har wa yau, a farkon watanni 9 na shekarar bana, yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a gabashin kasar Sin, da yankin tsakiyar kasar, da kuma yammacin kasar sun karu baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China