in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran: Ziyarar shugaban kasar Sin a wannan karo za ta kara zumunci tsakanin kasashen biyu
2016-01-18 11:35:40 cri
Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping zai fara ziyarar aikinsa a kasar Iran nan gaba cikin kwanaki masu zuwa bisa gayyatar da takwaransa na kasar Iran Hassan Rouhani ya yi masa.

Yayin wata hira da manema labarai, jakadan Sin dake kasar Iran Pang Sen ya bayyana cewa, zabar yankin gabas ta tsakiya a matsayin zangon farko na ziyarar shugaba Xi a wannan sabuwar shekara ta 2016, ya bayyana muhimmancin da Sin ke dorawa kan dangantakar dake tsakanin Sin da yankin gabas ta tsakiya, kuma hakan ya nuna kyakkyawar fata da dora babban muhimmanci ga bunkasuwar dangantaka dake tsakanin Sin da Iran a nan gaba.

Mista Pang ya kara da cewa, bangarorin biyu za su kai ga cimma matsaya daya kan wasu manyan batutuwa dake da nasaba da ciniki, da tattalin arziki tsakaninsu, tare da tabbatar da fannonin da za su yi hadin gwiwa nan gaba.

Ban da haka kuma, Sin da Iran za su sa hannu kan wasu yarjeniyoyi da takardun fahimtar juna a wasu manyan fannoni, ta yadda za su aza harsashe mai inganci ga hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin samar da kayayyaki, da tuntubar juna da mu'amala, da zuba jari, da man fetur da iskar gas, da makamashi. Sauran sun hada da harkokin gwadago, da cudanya, da sadarwa, da harkar kwastan da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China