Shugaba Xi ya yi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar yayin taron tsarin Internet na kasa da kasa da ke gudana a garin Wuzhen da ke lardin Zhejiang a nan kasar Sin.
Shugaban na kasar Sin ya kuma gabatar da shawarwari guda biyar muddin ana bukatar a ci gajiyar fasahar Internet.
Na farko, kamata ya yi a hanzarta samar da kayayyakin sadarwa na Internet da za su hade bangarori daban-daban waje guda, ta yadda za a rika musayar al'adu da koyi da juna.
Na biyu shi ne bullo da matakan tsaro kan yadda ake tafiyar da harkokin Intenet. Na uku, kamata ya yi kasashen duniya su bullo da matakan yin shawarwari da musayar ra'ayoyi ta yadda za a rika warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu kan harkar Internet, sai kuma nuna gaskiya da bin doka yayin ake kokarin gina al'umma ta gari ta wannan harka.
Bugu da kari shugaba Xi ya ce kamata ya yi a bullo da tsarin kula da harkokin Internet kamar yadda doka ta tanada.
Daga karshe shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta hada kai da dukkan kasashe wajen bullo da matakan yin shawarwari da musayar ra'ayoyi kan yadda za a warware bambance-bambancen dake tsakaninsu dangane da tsaron internet.(Ibrahim Yaya)