Game da hakan, jakadan Sin dake kasar Masar Song Aiguo, ya bayyawa wakilinmu a jiya Lahadi 17 ga wata cewa, a halin yanzu ana karfafa hadin kai da zumunta tsakanin sassan biyu, kuma ziyarar ta shugaba Xi Jinping a Masar, za ta sa kaimi ga inganta hadin gwiwar kasashen a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu, da ilmi, da yawon shakarawa da dai sauransu. Ya ce ta hakan za a bunkasa hadin gwiwarsu, da raya dangantakar abokantakar kasashen biyu daga dukkan fannoni. (Zainab)