Bayan faruwar bala'in, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada umurni ga hukumomin lardin Guangdong, da na birnin Shenzhen, da su gudanar da aikin ceto nan da nan, su kuma bada jinya ga mutanen da suka ji rauni, da jajantawa iyalan wadanda suka ji rauni ko suka bace. Ya ce ya kamata a gudanar da aikin ceto ta hanyar da ta dace, da magance sake faruwar bala'in.
Hukumomin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin, sun jagoranci hukumomin larduna da birane, wajen kara bincike a fannin magance bala'i da hadari, da tsara shirye-shirye, da tsarin bayar da gargadin kare kai, da aikin tsugunar da mutanen da bala'u suka shafa, don tabbatar da tsaron jama'a da na dukiyoyinsu.
A halin yanzu, ana gudanar da aikin ceto yadda ya kamata a yankin. (Zainab)