Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira wani taron bita a yayin rangadin aikin da ya kai birnin Chongqing a kwanan baya, inda ya saurari shawarwari da ra'ayoyi dangane da yadda za a kara kokarin bunkasa yankin tattalin arziki na kogin Yangtze.
A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kogin Yangtze, shi ne mahaifar al'ummar Sinawa, haka kuma babban ginshiki ne wajen raya al'ummar Sinawa. Don haka dole ne a yi la'akari da irin moriyar da al'ummar za su dade suna girba yayin da ake kokarin bunkasa yankin tattalin arziki na kogin. Bugu da kari, wajibi ne a mayar da hankali wajen kiyaye muhalli yayin da ake kokarin raya yankin, a kokarin cin gajiyar kyakkyawan muhalli tare da samun riba da alheri ga jama'a, ta yadda kogin na Yangtze zai yi ta bunkasa har abada. (Tasallah Yuan)