A safiyar yau Asabar, aka yi bikin kaddamar da bankin samar da jarin gina ababen more rayuwa na Asiya(AIIB) a nan birnin Beijing, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta.
A jawabinsa da ya gabatar, shugaba Xi ya bayyana cewa, bankin da aka kaddamar zai iya kara samar da jari ga ayyukan gina ababen more rayuwa a kasashen Asiya, tare kuma da sa kaimin cudanya da juna a yankin da kuma dunkulewar yankin baki daya, haka kuma zai kai ga kyautata yanayin zuba jari a kasashe maso tasowa da ke nahiyar ta Asiya da kuma samar da guraben aikin yi. Baya ga haka, bankin zai iya taimaka wa wajen farfado da tattalin arzikin Asiya da na duniya baki daya. Har wa yau, kaddamar da bankin na da muhimmiyar ma'ana ta fannin kyautata tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya.
Shugaban ya jaddada cewa, kasancewarta kasar da ta ba da shawarar kafa bankin, kasar ta Sin za ta ba da cikakken goyon baya ga bunkasa da kuma gudanar da shi, inda ban da biyan kudin da aka kayyade ba, za ta kuma samar da dala miliyan 50 ga asusun musamman da bankin za kafa, a yunkurin tallafa wa kasashe mambobin bankin da ke fama da karancin ci gaba wajen raya ababen more rayuwa.(Lubabatu)