Shugaba Xi ya ce kamata ya yi a kafa ginshikin dukkanin ayyukan da suka shafi wannan manufa, a shekaru uku na farkon ayyukan zurfafa gyare-gyare, sa'an nan a tabbatar da babbar taswirar manufofin gyare-gyaren cikin wannan shekara ta 2016.
Wata sanarwar bayan taron ta bayyana kiraye-kiyanen da mahalarta taron suka yi, game da gaggauta nazartar daukacin manufofin gyare-gyaren da ake aiwatarwa a dukkanin fannoni, da jera manufofin bisa muhimmancin kowannen su, tare da maida hankali kan muhimman lamura da ka iya taimakawa wajen aiwatar da gyare-gyaren yadda ya kamata.
Sanarwar ta kara da cewa, sauye sauye game da tsarin kamfanoni mallakar hukuma, da batun kudade da na haraji, da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, na kan gaba a fannin gudanar da gyaran fuska ga sha'anin ci gaba. Sauran sassan sun kunshi batun mallakar filaye, da bude kofa ga kasashen waje, da musayar al'adu da ilimi. Sai kuma batun samar da daidaito a fannin shari'a, da kare muhalli, da fansho ga ma'aikata, tare kuma da tsarin kiwon lafiya.