in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Saudiyya ya ce, ziyarar shugaban kasar Sin a Saudiyya zai ingiza dangantakar bangarorin biyu
2016-01-18 11:29:55 cri
Ofishin jakadancin Sin dake kasar Saudiyya ya shirya taron manema labaru a daren ranar 16 ga wata, inda aka sanar da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai a kasar Saudiyya.

Jakadan Sin a kasar Saudiyya Li Chengwen ya ce, wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin zai kai ziyara a kasar Saudiyya bayan da sarkin kasar Salman bin Abdulaziz Al Saud ya hau karagar mukami. Kasar Saudiyya kuwa ta kasance kasa ta farko a yankin Gabas ta tsakiya da shugaban Sin zai ziyarta.

Jakadan ya ce, makasudin ziyarar shi ne na kyautata dangantakar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. Li Chengwen ya fayyace cewa, a yayin ziyarar, shugaban kasar Sin zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Saudiyya, don tsara shirin raya dangantakar kasashen biyu, gami da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama. Ban da wannan kuma, shugabannin kasashen biyu za su yi musanyar ra'ayoyi game da manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya.

Tun daga ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyarar aiki a kasashen Saudiyya, Masar, da Iran. Kuma a matsayin ziyararsa ta farko a wannan sabuwar shekara, Saudiyya za ta kasance zagon farko da shugaban Xi zai fara ziyararta.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China