Xi Jinping ya bukaci a dauki matakan hana aukuwar munanan matsaloli a kasar
A kwanan baya ne, Mr. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin taron wakilan kwamitin dindindin na hukumar siyasa ta jam'iyyar, inda ya nemi a kara mai da hankali wajen yin rigakafin sake aukuwar munanan matsaloli yayin gudanar da aiki. Mr. Xi ya ce, darusan da aka koya a baya kamar asarar rayuka da zubar da jinin jama'a, wani gargadi cewa, wajibi ne a ba da muhimmanci wajen tabbatar da tsaron jama'a, har ila yau, dole ne a dauki matakan yin rigakafin aukuwar matsaloli a yayin da ake neman ci gaba, kuma dole ne a dauki matakan da suka dace na kawar da su domin tsaron jama'a da dukiyoyinsu. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku