in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Rasha sun taya juna murnar sabuwar shekara
2015-12-31 11:03:22 cri

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin suka zanta ta wayar tarho inda suka taya juna murnar sabuwar shekara.

A madadin gwamnati da jama'ar kasar, shugaba Xi Jinping ya taya shugaba Vladimir Putin da daukacin jama'ar kasar Rasha murnar sabuwar shekara da fatan alheri.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shekarar 2015, huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare ta bunkasa yadda ya kamata. Ya ce, yana fatan bangarorin biyu za su yi kokarin ci gaba da sada zumunta a tsakaninsu da kara imani da juna a fannin siyasa da nuna goyon baya ga juna, ta yadda sassan biyu za su amfana da juna bisa tushen kyakkyawar huldarsu a fannin siyasa, tare da kawo moriya ga jama'ar kasashen biyu har ma da sauran kasashen duniya.

A nasa bangare, shugaba Vladimir Putin na Rasha shi ma ya taya shugaba Xi Jinping da jama'ar kasar Rasha murnar sabuwar shekara, tare da fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata ga al'ummar Sin. Ya kara da cewa, a cikin shekarar 2015 da ke shirin karewa, kasashen Rasha da Sin sun gudanar da wasu manyan batutuwan hadin gwiwa. Yana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da tuntubar juna da yin hadin gwiwa domin inganta huldar dake tsakaninsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China