A yayin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar jaridar a ranar Jumma'a, mista Xi ya bayyana cewa ya kamata jaridar ta tallafawa ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma bin manufar jam'iyyar sau da kafa.
Shugaba Xi ya aike da wani sako bisa shafinsa na Weibo na jaridar, na fatan barka da sabuwar shekara ga dukkan mambobin rundunonin soja tare da basu kwarin gwiwa wajen kawo sabuwar gudunmuwa ga burin da lasar ta Sin lke neman cimmawa da kuma burinta na kafa wata rundunar soja mafi karfi.
Wanda aka kafa a ranar daya ga watan Janairun shekarar 1956, jaridar People's Liberation Army (PLA) Daily na bikin cikon shekaru 60.
Mista Xi ya bukaci jaridar da ta bayyana yadda ake gudanar da sauye sauye a yanzu haka ga ofisoshi da sojoji, musammun ma abin dake ciki da kuma manufar sauye sauye.
Haka kuma shugaba Xi, ya jaddada kawo kirkire kirkire a wannan zamani na internet da kuma yin kira ga jaridar da ta bi hanyar cigaba ta yanar gizo da kuma amfana da internet domin kyautata jaridar.
Har ila yau, ya yi kira ga 'yan jarida dasu rika zuwa wajen al'ummomi mafi talauci domin su ga yadda suke rayuwar yau da kullum.