Bisa sakamakon karshe da hukumar zaben ta fitar a jiya ranar Lahadi, jam'iyyar EPRD da jam'iyyun dake goyon bayanta, sun samu nasarar lashe kujeru 546 a cikin jimillar kujeru 547 na majalisar dokokin kasar, kuma ya zuwa yanzu ba a tabbatar da wace jam'iyya ce ta lashe sauran kujera daya tilo da ta rage ba.
An gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Habasha ne a ranar 24 ga watan Mayu, inda jam'iyyu 58, ciki har da EPRD mai mulki suka shiga takara.
Bisa tsarin mulkin kasar Habasha, jama'a na zaben mambobin majalissar dokokin kasar bisa wa'adin shekaru biyar-biyar. Kuma jam'iyyar dake da rinjayen kujerun majalissar kasar ce ke da ikon kafa majalissar ministocin kasar.
A zaben na wannan karo, wanda ya gabatakaron da ya gabata, wanda aka gudanar a cikin watan Mayu na shekarar 2010, hukumar zaben kasar ta tabbatar da cewa jam'iyyar EPRD ce ita ma ta yi rinjaye. (Zainab)