NEBE ta ce tuni ta yi rajistar masu kada kuri'u miliyan 36 da dubu dari takwas, tare da jam'iyyu 58 da za su fafata neman kujerun wakilci daban daban.
Kaza lika hukumar ta ce ta fara baiwa ma'aikatan zabe, da sauran masu ruwa da tsaki horo na musamman, baya ga ilmantar da masu kada kuri'u game da muhimman batutuwan da suka jibanci zaben da za ta gudanar. Duka dai da nufin cimma nasarar kammalar zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Bisa tsarin zaben dai jam'iyyun siyasa, da 'yan takara za su kammala yakin neman zaben ne a ranar 22 ga wata, wato kwanaki biyu ke nan kafin fara kada kuri'u.
Ana gudanar da manyan zabuka a kasar ta Habasha bayan shekaru biyar-biyar. Kuma zaben na bana zai zamo na 5, tun bayan kifar da gwanmnatin shugaba Derg a shekarar 1991.