Layin dogon mai amfani da lantarki ne kuma shi ne irin sa na farko da aka gina a nahiyar Afrika, yana da layuka biyu ne, sannan tsawon titin ya kai kilomita 34.
Tazarar titin daga arewa maso yamma wato daga kauyen Ayat, zuwa Tor Hailoch ya kai kilomita 17 da digo 34 ne, yayin da daga arewa maso yamma tsawonsa ya kai kilomita 16 da digo 9 wanda ya tashi daga Menelik II Square ya ratsa ta yankunan Merkato da Lideta da Legehar da Meskel Square da Gotera ya bulle zuwa Kaliti.
Kamfanin kasar Sin wato China Electric Power Equipment and Technology ne ya gudanar da aikin gina cibiyar sarrafa iskar gas wadda ke baiwa na'urar jirgin lantarki.
Da ma dai a watan Fabrairun wannan shekara, an gudanar da gwajin jirgin, yanzu kuma zai fara aiki gadan gadan bayan gudanar da kasaitaccen bikin budewa.
A lokacin kaddamar da sabon layin dogon, wanda ya samu halartar manyan jimi'an kasashen Habasha da Sin ministan sufurin kasar Workneh Gebeyehu, ya ce kammala wannan aiki mai matukar tarihi zai taimaka wajen inganta sha'anin sufuri ga kasar musamman a babban birnin kasar.
Ministan ya ce, yana taya kamfanin na kasar Sin murnar kammala aikin, sannan ya godewa al'ummar kasar ta Habasha bisa irin hadin kan da suke baiwa jami'an kamfanin lokacin gudanar da aikin.
Ya kara da cewar suna matukar alfahari da wannna aiki kasancewar zai taimaka wajen magance wahalhalun da ake fuskanta a harkar sufuri a bababn birnin kasar.
Shi dai wannan sabon layin dogo, yana da karfin daukar fasinja 300 a lokaci guda, kuma zai yi wa jama'a da ba su gaza dubu 60 ba aiki a kullum. (Ahmad)