in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasar Habasha a fannin al'adu
2015-12-08 15:58:04 cri
Mataimakin ministan al'adu na kasar Sin Yang Zhijin sun yi shawarwari da ministan al'adu da yawon shakatawa ta kasar Habasha Aicha Mohamed a jiya Litinin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara yin musayar ra'ayi da hadin gwiwa tare da kasar Habasha a fannin raya al'adu.

Yang, wanda ya kai ziyarar aiki a kasar Habasha tare da tawagar jami'an hukumar raya al'adu ta gwamnatin Sin wadda ke karkashin jagorancinsa. Ya ce, kasar Sin da Habasha suna da dankon zumunci na tsawon lokaci, shugabannin hukumomin raya al'adu na kasashen biyu, sun kara gudanar da musayar ra'ayoyi ne tun a shekarun baya, hakan aka inganta huldar dake tsakanin su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China