Taron kashi na farko da na biyu an yi su ne a biranen Monterrey na kasar Mexico da Doha na kasar Qatar sannan wannan karon taron na EFD za'a yi shi ne tsakanin ranakun 13 zuwa 16 a watan Yulin a Birnin Adis Ababa na kasar Habasha dake gabashin Afrika.
Ana sa ran taron zai dora akan wadanda aka yi a baya ya kuma amince akan manufa na ta gaba game da yadda cigaba zai samu bayan wa'adin 2015 , ganin yadda kasashen duniya suka amince shirin muradun karni na MDD zai kammala a karshen wannan shekarar.
Ganin an fara shirin taron, Habasha tana aiki tukuru domin samun nasarar daukan bacon bakuncin shirin na kwanaki hudu ta kowane bangare kamar yadda ma'aikatar kudi da cigaban tattalin arziki na kasar ta tabbatar.(Fatiamah Jibril)