A cewar wata sanarwar da aka fitar bayan wannan ganawa, tattaunawar bangarorin biyu ta fi mai da hankali kan batutuwan dake da nasaba da dunkulewar tattalin arziki da al'umma dake tsakanin kasashen biyu. Gano da hanyoyin fadada huldar dangantaka, musammmun ma a fannonin da suka shafi yaki da ta'addanci, da kuma wajibcin bunkasa dunkulewar shiyyar domin tabbatar da zaman lafiya a yankin kusuwar Afrika da ma gabashin Afrika baki daya sun kasance cikin tattaunawa tsakanin shugaba Guelleh da firaministan kasar Habasha.
Haka kuma a cewar wannan sanarwa, za'a sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama a yayin ziyarar aikin faraministan kasar Habasha a Djibouti domin karfafa dangantakar tattalin arziki da al'umma tsakanin kasashen biyu, da kuma karfafa matsayinsu a shiyyar. Dukkan wadannan yarjejeniyoyi da za'a rattaba wa hannu an tsara su da kuma amincewa da su a yayin zaman taron kwamitin hadin gwiwa na kwararrun kasashen Djibouti da Habasha karo na 13 da aka kammala shi a ranar Laraba da ta gabata a kasar Djibouti. (Maman Ada)