Wakilin shugaban kasar Sin, kuma ministan kudin kasar Lou Jiwei, ya halarci taro karo na uku na kasashen duniya da MDD ta shirya, domin samar da kudade da kudurorin bunkasuwa. Taron dai ya gudana ne a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Cikin jawabin da ya gabatar, mista Lou ya ce samar da kudade da ayyukan bunkasuwa, muhimman abubuwa ne dake cikin kudurorin taron koli, na samar da ci gaba wanda MDD za ta gabatar a watan Satumbar shekarar nan ta bana. Kana yana cikin ajandar kudurorin ci gaba da aka tsara aiwatarwa bayan shekarar 2015.
Ban da wannan, mista Lou ya jaddada cewa Sin na dukufa matuka game da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, kuma tana kokarin gudanar da wannan babban aiki yadda ya kamata.
Tun lokacin da aka kira irin wannan taro a karon farko a shekarar 2002, Sin ta samar da kudade, da kasuwanni, da dabarun kimiya da fasahohi da dai sauransu ga kasashe masu tasowa, bisa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen masu tasowa. (Amina)