Kamfanin samar da na'urorin lantarki na kasar Sin, ya kammala aikin hada jiragen kasa da za su rika sufuri a kasar Habasha da wutar lantarki.
Rahotanni daga Kasar sun nuna cewa ya zuwa ranar Lahadin data gabata, an kammala dukkanin ayyukan samar da lantarki ga jiragen kasan wadanda za a yi amfani da su a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar ta Habasha.
Yayin bikin kammala wannan aiki da ya gudana a daya daga tashoshin jirgin, mataimakin firaministan kasar ta Habasha Debretsion Gebremikael, ya ce kammala aikin ya share fagen fara amfani da jiragen kasa a sassan birnin na Addis Ababa a hukunce. (Lami)