in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha na kokarin hadin gwiwa da kasar Sin
2015-10-29 14:07:48 cri

Mataimakin jakadan Habasha dake kasar Sin Mista Tesfaye Yilma Sabo ya shedawa manema labaru a jiya Laraba cewa, kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na kasar Sin zai fara zirga-zirga daga birnin Beijing zuwa Addis Ababa, ban da wannan kuma, kasahen biyu sun gina wani layin dogo mai saurin tafiya na zamani da aka fara amfani da shi yanzu haka a Habasha. Ya ce, kasar Habasha na kokarin amfani da wannan layin dogo a matsayin muhimminyar kafa ga Sinawa masu yawon shakawa zuwa nahiyar Afrika.

Mista Tesfaye ya kara da cewa, Habasha na daukar kasar Sin a matsayin sahihiyar abokiyar hadin gwiwa, tana kuma fatan kara hada kai da Sin a fannoni daban-daban ciki hadda aikin noma, manyan ababen more rayuwa da dai sauransu. A cewarsa, akwai kwanciyar hankalin siyasa da yanayi da manufofi masu kyau wajen shigo da jari kasar Habasha. Haka kuma akwai kwadago da dama, don haka tana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar.

Habasha na samun karuwar tattalin arziki a 'yan shekarun baya-baya nan, Habasha wadda ake mata lakabi da "Kolin nahiyar Afrika" na da karfi sosai ta fuskar tattalin arziki. Mista Tesfaye ya ce, muhimmin aiki da aka sa gaba shi ne kawar da talauci, Habasha za ta koyi nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raya sana'ar samar da kayayyaki da yadda masana'antu za su taimaka wa jama'ar kasar wajen kawar da talauci.

A watan Nuwamban bana ne za a cika shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Habasha. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China