Bisa wannan shiri, yawan karuwar tattalin arzikin kasar a farkon shekaru hudu zai kai kashi 10.1 bisa dari, daga cikinsu aikin noma zai samu karuwar kashi 6 bisa dari, yayin da sha'anin ba da hidima zai samu karuwar kashi 10.7 bisa dari, a sha'anin kere-kere kuwa, za a samu karuwar kashi 13 bisa dari. Ban da haka kuma, aikin ba da ilmi, da aikin ba da jiyya da dai sauransu, za su samu bunkasuwa yadda ya kamata.
NPC kuwa ya ce, za a dauki matakai don tinkarar matsalar rashin samun bunkasuwa mai kyau a sha'anin kere-kere bisa shirin GTP, ta yadda wannan sha'ani zai kara ba da gudummawarsa a cikin shirin GTP-II.
Ban da haka kuma, hukumar kiwon lafiya ta kasar Habasha ta ba da labarin cewa, kasarta ta cimma nasarar kammala aikin kiwon lafiya dake cikin shirin GTP, da kuma muradun karni na MDD wato MDGs. Inda yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, da yaduwar cutar sida ya ragu da kashi 90 cikin dari bisa na shekarar 2010, yayin da yawan likitoci ya karu zuwa 9000, matakin da ya nuna cewa, mutane dubu 40 na iya samun ganin likita daya tak a da, inda a yanzu kuwa mutane dubu 10 ke iya samun ganin likita guda. (Amina)