Li, ya ce koda yake wannan batu ba wani boyayyan al'amari ba ne idan aka yi la'akari da irin jajurcewa da kuma tsayawa kai da fata da kasar ke yi don ganin an samar da kyakkywar makoma wajen habaka cigaban tattalin arzikin kasar a nan gaba.
Wasu daga cikin manyan matakan da kasar Sin ta fara dauka na habaka tattalin arzikin sun hada da sake bunkasa cigaban masana'antu da fasahar sadarwa da raya birane da kuma bunkasa aikin gona irin na zamani, dukkannin wadannan matakai za su samar da abubuwan bukatun yau da kullum ga al'ummar kasar.
Li, ya kara da cewar, nau'ika dabam dabam na masana'antu da kasar Sin ke da su za su iya kasancewa a matsayin abin dogaro na yiwuwar bunkasar cigaban tattalin arzikin kasar a nan gaba.
Sa'an nan ya kara da cewar shirin sake fasalin tattalin arziki da kasar ta bullo da shi ya samu gagarumar nasara.
Ya ce kasancewar kasar Sin ita ce kasa dake kan gaba a duniya wajen cigaba, zata cigaba da daukar ingantataun matakan da zasu tabbatar da dorewar cigaban da kasar ke samu.
Li ya yi Karin haske dangane da shirin garambawul a sha'anin kudade kasar inda ya jaddada muhimmancin kiyaye tsarin dokar harkokin cinikayya a matsayin wani bangare da zai tabbatar da aza tubalin cigaban tattalin arzikin a kyakkyawan yanayi da kuma kaucewa fadawa cikin barazanar karayar tattalin arziki.
Kazalika makudan kudaden da kasar Sin ke adawa a asusun ajiyar ta na kasashen waje na matukar taka rawa wajen daidaita tattalin arzikin kasar, in ji firaministan.(Ahmad Fagam)